Tsohuwa mai shekaru 102 zata fito takarar shugan ƙasar Najeriya a 2023

Wata tsohuwa mai shekaru 102 ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar Shugabancin Najeriya a kakar zaɓe mai zuwa na 2023.

Ƴar shekaru102, Misis Nonye Josephine Ezeanyaeche,ta ce tana da tsare-tsare masu kyau ga Najeriya idan ta zama shugaban kasa a 2023.

Ezeanyaeche, wacce ake kira ‘Living Legend’ ‘Mama Africa ita ce ta kafa kungiyar ‘Voice for Senior Citizens of Nigeria’
kuma ta fito ne daga Aguata a jihar Anambra.

Popular News Hausa ta ce ta ji majiyarta ta Leadership Newspaper ta ruwaito cewa matar ta fito ne a wata ziyarar da ta kai wa tawagar gudanarwa na hukumar Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) kwanan nan, inda ta bayyana shirin tsayawa takarar mukamin idan har matasan kasar nan ba su shirya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram