Akwai Jahilci Da Rashin Hankali Cikin Ƴan Majalisar Dokokin Jahar Zamfara – In Ji Mataimakin Gwamnan Jahar

Mataimakin gwaman jahar Zamfara, Mahdi Aliyu ya ce akwai jahilici da rashin hankali danga ne da danbarwar da ke faruwa tsakaninshi da yan majalisar dokokin jahar.

Mahdi Aliyu ya faɗi haka ne a cikin wani hoton bidiyo da BBC Hausa ta saki a shafinnta na Facebook a wata fira da ta yi da shi dangane da batun.

Ya ce komai akwai yadda kundin tsarin mulki ya tanadi a yi shi, to amma su yan majalisar dokokin jahar ba sa bin wannan tsari.

Ya ce kundin tsarin mulkin ya yi bayani dalla-dalla yadda ake tsige mataimakin gwamna koma gwamnan.

Aliyu ya ce tun farko abinda ya kamata su yi shine su turo mashi takarda kai tsaye to amma basu yi haka ba sai suka sanya sakataren gwamnati ya rubuta mashi ya bashi don haka ya ce tun anan an karya doka.

Ya ce irin wannan rashin iliminn da jahilci ya sanya bai saurari kiransu ba ma.

Mataimakin gwamna ya bada misali da cewa lokacin da gaba dayansu suna PDP ai ba su suka ci zaɓe ba amma saboda APC ba ta yi abinda ya dace ba kotu ta kwace mulkin ta mika masu, to yanzu kuma abinda suke yi kotu ta yi umurni da a dakata amma sun ki sauraron kotu don haka ya ce wannan ba komai ba ne in ba jahilci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram