Tinubu Ya Faɗa Ma Matasa Shine Kan Layi Wanda Zai Zama Shugaban Ƙasa Kafi Su

Tsohon gwamnan Legas kuma jagoran jam’iyya mai mulki a Najeriya ta APC, Bola Ahmed Tinubu ya ce ma matasan ƙasar cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai idan shi ya yi tukuna.

Tinubu ya faɗi haka ne a yayin wata ziyara da ya kai wa Alaafin na Oyo Lamidi Adeyemi, a ranar Lahadin nan da ta gabata.

Fitaccen lan siyasar ya buƙaci matasa da su ba magabatansu dama.

BBC ta naƙalto inda Tinubu ke cewa, “Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ƙasa, idan kun zama shugaban ƙasa fa, za ku kore mu ne a gari?”

“Sai kun tsufa za ku zama shugaban ƙasa, kuma sai na riga zama shugaban ƙasa,” in ji Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram