Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga babar jam’iyyar awada, PDP tare da ɗumbin magoya bayansa.
Gwamnan ya sanar da ficewar ta sa ne a wurin wani taron masu ruwa da tsaki na kafa wata sabuwar ƙungiyar masu kishin ƙasa mai suna “The National Movement” da ya gudana a babban ɗakin taro na “National Conference Center” da ke birnin tarayya Abuja.
Kakaki Network ta ruwaito cewa daga majiyarta ta Nigerian News Hausa da ta wallafa a shafinta cewa, Ƙungiyar ta ƙunshi manyan jiga-jigan ƴan siyasa da ƴan kasuwa da kuma ƙungiyoyin fararen hula.