Da Ɗumi- Dumi: Kotu Ta Amince Da Bukatar NDLEA Na Tsare Abba Kyari Na Tsawon Kwanaki 14

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA na tsare mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari na tsawon kwanaki 14.

An tsare Kyari tun ranar 14 ga Fabrairu, shekarar 2022, bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Iza Ƙeyar Wani Mutum Zuwa Gidan Gyaran Hali Saboda Ya Ƙara Aure Ba Tare Da Yardar Matarshi Ba

A kotun a ranar Talata, NDLEA, ta bakin lauyanta, Mike Kassa, ya bayar da hujjar ba da karin lokaci domin kammala binciken domin shari’ar madakalar miyakun kwayoyin na da sarkakiya, kuma tana iya bukatar hukumar ta fita zuwa gabar tekun Najeriya a yayin gudanar da bincikenta.

Da yake bayar da bukatar, alkalin ya ba da umarnin cewa za a kirga wa’adin kwanaki 14 daga ranar 22 ga Fabrairu.

Mai shari’a Zainab Abubakar ta ce wannan lokaci ne domin baiwa hukumar damar kammala bincike kan lamarin.

Kyari dai ya shigar da kara ne a ranar litinin da ta gabata, inda ya nemi a bi masa hakkinsa.

Ya roki kotu da ta sake shi saboda rashin lafiya, saboda yana da ciwon suga da hawan jini.

Amma alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraron belin har zuwa ranar Alhamis

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram