Kotu Ta Amince A kori Jami’ar Ƴar Sanda Da Ta Ɗauki Ciki Ba Ta Hanyar Aure Ba.

Wata babbar kotun tarayyar Najeriya ta amince da matakin da rundunar ƴan sandan ƙasar ta ɗauka na korar wata jami’ar da ta ɗauki ciki a shekarar da ta gabata.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, mai shari’a Inyang Ekwo ya ce bai ga wani gamsashshen dalili ba na “haifar da ruɗani ga tsarin rundunar ba”.

Ya ƙara da cewa “Duk wanda da ya shiga rundunar dole ne ya kiyaye dokokinta ko kuma kada ya shiga rundunar saboda babu tilas game da zama mambanta.”

Ƙungiyar lauyoyin Najeriya ce ta shigar da ƙarar bayan korar wata jami’ar ƴan sanda ta yi ciki ba ta da aure a watan Janairun 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram