Kotu Ta Iza Ƙeyar Wani Mutum Zuwa Gidan Gyaran Hali Saboda Ya Ƙara Aure Ba Tare Da Yardar Matarshi Ba

Wata kotu a Ƙasar Pakistan ta ɗaure wani mutum tsawon watanni shida a gidan yari saboda ya ƙara aure ba tare da amincewar matarsa ba.

Kotun dake da mazauni a Lahore ta yi watsi da iƙirarin mutumin mai suna Saqib cewa addininsa ya ba shi ƴanci a matsayinsa na musulmi.

BBC Hausa ta ruwito cewa, matarsa Ayesha Bibi, ta samu nasara ne a kotun, bayan ta yi faɗi cewa ƙarin auren ba tare da amincewarta ba ya saɓa wa dokar iyali ta Pakistan.

Kotun ta ci tarar mijin dala dubu biyu.

Masu fafutikar kare haƙƙin mata, sun ce hukuncin zai karya guiwar mazan da ke da niyyar ƙarin aure, kuma zai buɗe wa mata ƙofar kai mazajensu kotu.

A Pakistan maza na auren fiye da mata ɗaya, amma dole sai namiji ya nemi amincewar matarsa ta farko kafin ya auri ta biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram