Najeriya Na Da kayayyakin Da Ake Muƙata Domin Samar Da Maganin Cutar Covid-19 — Masani

Dr Okai Aku, Babban Daraktan Hukumar PPFN a ranar Talata yace Najeriya nada Masana, da Kayayyakin Ai domin samar da maganin cutar Covid-19.

Mr Aku Masani a ɓangaren lafiya, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a Abuja.

Idan dai za’a tuna, Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO, ta sanar da cewa Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe 6 da zasu karɓi gudunmawa ta samar da maganin cutar Covid-19.

KARANTA WANNAN LABARI:Da Ɗumi- Dumi: Kotu Ta Amince Da Bukatar NDLEA Na Tsare Abba Kyari Na Tsawon Kwanaki 14

Sauran Ƙasashen sun ƙunshi Egypt, da Kenya, da Senegal, da Afirka ta Kudu, da kuma Tunisia.

A lokacin da yake yabawa Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko akan taimakon, Mr Aku yace “Najeriya nada dukkanin abinda ake buƙata domin ta samar da magani, ina da tabbacin zamu iya.

“Koda babu Ma’aikata, zamu iya samar da Fasaha daga wasu ƙasashe domin yin maganin.”

Daraktan Hukumar ta PPFN yace dogaro da sauran ƙasashe domin samar da cutar Covid-19 zai taimaka wajen cigaban Lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram