Nan Da Awanni Kaɗan Buhari Zai Rattaba Hannu Kan Dokar Zaɓe – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban kasa ta ba da tabbacin cewa nan da sa’o’i kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rattaba hannu a kan kudirin gyaran dokar zabe da aka sake yi.

Mista Femi Adesina, mai ba shugaba Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya bayyana a shirin gidan Talabijin na Channels, Sunrise Daily.

Ya ce, “Za a iya sanya hannu a yau; ana iya sa hannu a gobe. A cikin sa’o’i kadan, ba kwanaki ba. Awanni na iya zama sa’o’i 24, yana iya zama sa’o’i 48; ba kwanaki ba, ba Kuma makonni ba.”

DAILY POST ta tuna cewa bayan gyara dokar da ta janyo cece-kuce, majalisar dokokin kasar a ranar 31 ga watan Junairu, 2022, ta mika wa bangaren zartarwa don sanya hannu a kan dokar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram