Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan yi Dr Chris Ngige ya ɗage taron sa da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU da aka sanya ƙarfe 1 na ranar Talata 22 ga watan Fabrairu na shekarar 2022 zuwa ƙarfe 2 na rana, kamar yadda Jaridar The PUNCH ta ruwaito.
Mai Magana da Yawun Ma’aikatar Ƙwadago da Samar da Ayyukan yi Charles Akpan ya bayyana haka a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN:Nan Da Awanni Kaɗan Buhari Zai Rattaba Hannu Kan Dokar Zaɓe – Fadar Shugaban Ƙasa
Duk da Akpan bai bayyana dalilan da suka sanya aka canja lokaci, amma Wakilin Majiyar mu ya gano cewa, Ma’aikatar naso ta sanya komai akan ƙa’ida kafin ganawa da Ƙungiyar.
Ngige dai ya sanya ƙarfe 1 na ranar Talata domin taro da Shuwagabancin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU a ofishin sa dake Ma’aikatar Ƙwadago da Samar da Ayyukan yi, Abuja.
Manufar taron kamar yadda rahotanni suka bayyana, shine a fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya da ASUU.
ƙungiyar ASUU a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022 ta ayyana yajin aiki na makonni 4, akan kasawar Gwamnati na cika masu wasu alƙawurra da tayi da Ƙungiyar.