Ƴan Fashin Yanar Zigo Sun Yi Garkuwa Da Wasu Shafuka Har Sun Buƙaci Dala Dubu 20 A Matsayin Kuɗin Fansa

Wasu da ake kyautata zaton masu kutse ne ta intanet sun ƙwace iko da shafuka 34 na ƙasar Mozambique jim kaɗan bayan gwamnatin ƙasar ta ce ta daƙile irin wannan harin a ranar Litinin.

Wata ƙungiya da ake kira “Yemeni Hackers” ta yi iƙirarin cewa ita ta yi kutsen.

KARANTA WANNAN LABARIN:Ba Gobara Ba Ce Ta Tashi, Batira Ne Suka Kama Da Wuta A Hedikwatar Kuɗi.

Daga cikin shafukan intanet da aka yi wa kutsen sun haɗa da na hukumomin kiyaye afkuwar bala’i da hanyoyi da ruwa da kuma tsaro.

Kakaki Network ta ce, BBC Hausa ta ruwaito cewa masu kutsen sun ajiye saƙo a ɗaya daga cikin shafukan da suka yi wa kutsen inda suka buƙaci a biya su kuɗin fansa cikin sa’o’i 24 kafin su saki shafin.

Sannan sun ce, suna buƙatar a biya su dala dubu 20 ta hanyar bitcoin idan kuma ba haka ba sun ce za su wallafa bayanan sirri na ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram