Gwamnan jahar Katsina Aminu Masari, ya bada filaye 20 ga gwamnatin tarayya domin gina wuraren sayar da iskar gas.
Gwamnan Masari ya bada umurnin a ba gwamnatin tarayya filayen ne a ranar Talatar nan da ta gabata a yayin taron wayar da kan al’umma na kwana 1 da Ofishin mataimakin shugaban ƙasa ya shirya a ƙarƙashin shirin faɗaɗa hanyar amfani da iskar gas a matsayin makamashi da ya gudana a babban ɗakin taro na Sakatariyar jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Ɗumi-Ɗumi: Gobara Ta Tashi A Hedikwatar Ma’aikatar Kuɗi Ta Najeriya
Masari wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jahar Mustapha Inuwa ya yaba ma gwamnatin tarayya bisa ɓullo da tsarin wanda yana ɗaya daga cikin hanyoyin da ke nuna muhimmancin sauran albarkatun man fetur da ya kamata a mayar da hankali kansu.
Kakaki Network ta ce, gangamin an yi mashi take da “Shawo kan matsalar tattalin arziƙi da inganta rayuwar al’umma jahar Katsina ta hanyar amfani da sinadarin iskar gas.”
Mr Dayo Adeshina mai ba mataimakin shugaban ƙasa shawara na musamman wanda shi ne ya wakilci mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa bayan amfani da gas wajen yin girki za kuma a iya amfani da shi ta fuskar haɓɓaka tattalin arziƙin jahar.