Yan majalisar dokokin jahar Zamfara sun amince da naɗin Sanata Hassan Nasiha a matsayin sabon mataimakin gwamnan jahar jim kaɗan bayan tsige mataimakin gwamnan Mahdi Aliyu Gusau.
Sanata Hassan Nasiha wanda shine ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Zamfara ta tsakiya a majalisar Dattawa ta Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan Majalisar Dokokin Jahar Zamfara Sun Tsige Mataimakin Gwamnan Jahar Mahdi Aliyu
An tabbatar masa da zama mataimakin gwamnan ne ba tare da wasu tambayoyi ba daga ƴan majalisar.