An rantsar da Sabon mataimakin gwamnan Zamfara Sanata Hassan Muhammad Nasiha.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kocin Ƙungiyar Mirandes Ya Koka Kan Yadda Sadiq Na Super Eagles Ya Jefa Ma Ƙungiyar Ƙwallaye 2
Alƙaliyar Alƙalai ta Zamfara Kulu Aliyu ce ta rantsar da sanatan a yau Laraba bayan da ‘yan majalisar dokokin jihar sun tsige Mahdi Aliyu Gusau daga muƙamin mataimakin gwamnan.
BBC Hausa ta ce, a yau Laraba ne Kakakin Majalisar Dokoki Nasiru Muazu Magarya ya karanta wasiƙar da Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya aike musu ta neman tantancewa da naɗa Sanata Nasiha a matsayin mataimakinsa.