Kocin Ƙungiyar Mirandes Ya Koka Kan Yadda Sadiq Na Super Eagles Ya Jefa Ma Ƙungiyar Ƙwallaye 2

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Mirandes da ke rukuni na 2 a kasar Spain, Etxeberria, ya koka a kan yadda dan wasan Super Eagles, Sadiq Umar ya jefa wa kungiyar sa kwallaye biyu.

Umar din ya yi nasarar cin kwallayen biyu ne a yayin da kungiyar sa ta Almeria ta doke Mirandes din da ci 2-1.

Wannan ita ce nasara ta uku a jere da Almeria ta samu tun bayan dawowar dan Najeriyar daga gasar cin kofin kasashen Afirka, AFCON.

KARANTA WANNAN LABARIN:Ƴan Fashin Yanar Zigo Sun Yi Garkuwa Da Wasu Shafuka Har Sun Buƙaci Dala Dubu 20 A Matsayin Kuɗin Fansa

Tun kafin wasan na mako na 28 ne dai Etxeberria ya bayyana Sadiq Umar a matsayin dan wasan Almeria ma fi hadari tare da shan alwashin daukar matakin hana shi hasala komai.

Umar dai ya nuna wa Etxeberria cewa shi ba kanwar lasa ba ne inda ya jefa kwallaye biyun da suka bai wa kungiyar sa ta Almeria nasara a kan Mirandes da ci 2-1.

Kociyan Mirandes din dai ya ce, babu abin da ‘yan wasan bayan sa ba su yi ba na su hana Umar haskawa amma hakan ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram