Saudiyya Zata Samar Da Ruwan Sha Ga Mutane 628,832 A Nijar

Ƙasar Saudiyya a ƙarƙashin asusun bada agaji na Sarki Salman zata tona fanfon tuƙa-tuƙa guda 241 a jamhuriyar Nijar.

Jarjejeniyar haƙa rijiyoyin na da nufin samar da su ne ga mutane 628,832 da ake sa ran zasu amfana.

Injiniya Ahmed bin Ali Al-Bees, wanda shi ne shugaban asusun ya sanya hannu akan yarjejeniyar a hedikwatar ƙungiyar da ke cikin birnin Riyadh.

KARANTA WANNAN LABARIN: An Rantsar Da Sabon Mataimakin Gwamnan Zamfara, Satana Nasiha.

A wata sanarwa da kamfanin dillanci labarai na Saudiyya ya ruwaito cewa darakta mai kula da sashen lafiya da mujalli na asusun, Dr. Abdullahi Al–Muhallem, ya ce sun sanya hannu akan kwangilar da za ta taimaka ma Nijar haƙa rijiya 241 masu zurfin mita 20-30.

Ya ce kuma wannan wani yunƙuri ne na samar ma mutane wadatacce kuma tsabtataccen ruwan sha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram