Ƴan Zanga-Zanga Sun Kusa Afka Ma Gidan Hadimin Masari A Katsina

A Ranar Larabar nan ne wasu mutane a garin Sabon Garin Malam Yahuza da ke kan hanyar Batsari a cikin ƙaramar hukumar Batagarawa suka yi zanga-zangar nuna rashin jin daɗinsu dangane da aikace-aikacen ƴan ta’adda da ke ƙara addabar garin.

Lamarin ya faru ne bayan da ƴan bindiga suka ziyarci gidan wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Abu Mai Bulawus
da ke zaune a garin na Sabon Garin Yahuza a cikin tsakiyar daren ranar Talata kuma suka she shi har lahira.

KARANTA WANNAN LABARIN: Saudiyya Zata Samar Da Ruwan Sha Ga Mutane 628,832 A Nijar

Lamarin da ya ƙara harzuwa ƙa yan garin har suka ɗaukin matakin yin zanga-zanga domin nuna damuwarsu inda suka fito suka rufi babban titin tare da ƙona tayoyi.

Hahazalika a yayin zanga-zangar an ƙone shingen jami’an tsaron farin kaya na Sibildifen wanda yana daidai gaban wani gini da mutanen garin suka shida ma Jakadiya cewa na wani babban mai hidimta ma gwamnan jahar ne.

Wani mutum da ya buƙaci da a ɓoye sunanshi ya ce masu zanga-zangar har sun yi niyar shiga gidan sai shi mai kula da gidan ya samu ya shawo kansu suka haƙura.

Saidai wasu matasa a ɗayan ɓangaren sun musanta cewa masu zanga-zangar sun yi niyar shiga gidan su yi ɓarna.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da yan fashin daji ke zuwa kai hari a Sabo Garin na Malam Yahuza ba.

Sabon Garin Malam Yahuza dai a yanzu shi ne gari na farko da ake fara taras wa indan mutum ya bar cikin birni Katsina ya nufi hanyar ƙaramar hukumar Batsari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram