Babban Bankin Duniya Sha Alwashin Kowane Yaro Sai Ya Samu Ilimin Zamani Da Ingantattar Lafiya A Katsina

Babban bankin Duniya ya ƙuduri aniyar taimakawa Gwamnatin Jihar Katsina wajen tabbatar da ganin cewa kowanne yaro ya Samu ingantaccen ilimin zamani da kuma ingantacciyar lafiya.

KARANTA WANNAN LABARIN: Nan Gaba Zamu Ɗauki Mataki Kan Masu Gidajen Man Fetur Da Ke Sayar Da Lita Fiye Da 165 A Katsina

Babban Daraktan Bankin a Najeriya, Farfesa Shubhan Chaudhuri ne ya sanar da haka a ranar Larabar nan da ta gabata a yayin ziyarar sa da ya kawo a jihar Katsina tare da sauran ƴan tawagar sa domin duba ayyukan da hukumar NEWMAP ke aiwatarwa a wurare daban daban da matsalar ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Kakaki Network ta ruwaito, cewa, Farfesa Chaudhuri ya kuma ƙara bada tabbacin shirin Babban Bankin na gina hanyoyi a jihar domin samar wa manoma hanyoyi da zasu sada su da kasuwanni cikin sauƙi tare da ɓullo da hanyoyin da zasu inganta tattalin arziki ga matasa tare da fitar da al’umma daga ƙangin talauci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram