Matsalar Tsaro A Yankin Arewa, Auren Wuri Ne Ya Haddasa Shi — Sanata Odebiyi

Sanata mai Wakiltar Ogun ta Yamma ya bayyana damuwar sa akan yawaitar Kashe-Kashe, da kuɗin fansa, da fyaɗe, da dukkanin matsalolin tsaro dake fuskantar yankin Arewa na Najeriya.

Ya bayyana wannan matsalar ta’addanci a matsayin Auren wuri wanda ya zamanto Al’adar yankin Arewa, yana mai cewa, sai an daina Auren Wuri, sannan za’a magance talauci.

KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Isa Lafiya Ta Jihar Nasarawa A Ziyarar Kwana Biyu

Ya bayyana haka, a lokacin da yake bada gudunmawar shi a waj ƙudiri da aka gabatar mai taken “buƙatar dake akwai na magance kisan ƴan ta’adda da sauran matsalolin tsaro a Ƙananan Hukumomi na Wasagu-Danko da Sakaba na Jahar Kebbi,” wanda Sanata Bala Ibn’Nallah mai wakiltar Kebbi ta Kudu ya gabatar a ranar Laraba.

A gudunmuwar shi, Sanata Odebiyi ya bayyana cewar yawaitar matsalar tsaro a Arewa zai cigaba saboda wani mataki da aka ɗauka na maganin matsalar, marar ɗorewa, tana mai cewa magance matsalar tsaro a Arewa, sai an magance matsalar daga tushe.

A cewar sa “a lokacin da Auren wuri yana faruwa sabudda talauci”, sai suka haifi yaro a wannan yanayi, da zaran ya girma, to ƴan ta’adda sai su ɗauke su aiki.

Sanatan ya koka kan yawaitar yara marasa zuwa Makaranta, yana mai cewa a shekaru 9 Najeriya ta samu mutane Miliyan 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram