Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa a ziyarar aiki ta kwanaki biyu.
Shugaban wanda ya zo a cikin jirgi mai saukar ungulu kirar 5N-FG2 ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na jihar Nasarawa da misalin karfe 10 na safe.
A filin jirgin dai wadanda zasu tarbi shugaba Buhari akwai gwamnan mai masaukin baki, Abdulahi Sule, gwamnonin jihohin Kogi da Kebbi, Yahaya Bello da Atiku Bagudu da mataimakin gwamnan jihar Benue da dai sauransu.
Wasu daga cikin ayyukan da za a kaddamar sun hada da sabon babban bankin Najeriya, CBN, wani gini da karamar tashar wutar lantarki.