Uzodimma Kasawa Ce Arha Ɓagas, PDP Zata Karɓie Jahar Imo — inji Wike

Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike a ranar Laraba, yace Gwamnan Jahar Imo Hope Uzodimma ya faɗi ƙasa kwata-kwata.

Yace irin gazawar sa, ya sanya cikin ruwan sanyi PDP zata karɓi mulkin Jahar a Babban zaɓe mai zuwa na Shekarar 2023.

Gwamna Wike ya bayyana haka a Babban wani Shagalin Biki domin girmama Sakataren Jam’iyyar PDP Sanata Samuel Anyanwu, Wanda Jam’iyyar PDP reshen Owerri ta shirya a ranar Laraba.

Gwamna Wike yace yazo taron Shagalin ne, domin ya jaddada bukatar dake akwai na Jam’iyyar PDP ta shirya tare da karɓe kujerar Gwamnan Jahar Imo.

“Kuskuren da zamu yi da zamu bari wannan mutumen ya dawo shine, muki yin aiki a tare, kuma bazamu yi wannan kuskuren ba.

“Yanzu, dole mu haɗa kai. Idan babu Jam’iyya, to babu Gwamna. Idan babu Jam’iyya, babu Shugaban Ƙasa.

“Kada muji tsoro, babu wanda zai iya ci mana zarafi, lokaci ya wuce, da wani zai ɗauki na huɗu, kuma ya zaman to na farko. Bazai taɓa faruwa ba,” inji shi.

Wike a lokacin taron ya kuma, yiwa APC dariya, data ɗage zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙasa daga ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa 26 ga watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram