Ƴansanda Sun Ce Sun Kama Wani Direba Da Suke Zargin Yana Ɗaukar Ƴan ta’adda Da Motarsa Ya Kai Su Wurin Da Zasu Saci Mutane A Katsina.

Rundunar ƴansandan jahar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kama wani direba mai wata da ake zargin yana haɗa baki da ɓarayin daji ya ɗauko su zo su saci mutane.

Mai magana da yawun rundunuar SP Gambo Isah ne ya ganatar da wanda ake tuhuma gaban manema labarai a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a farfajiyar hedikwatarsu da ke Katsina.

Wanda ake zargin mai suna Shamsu Ɗahiru mai shekaru 36 ɗan asalin ƙaramar hukuma Funtua, a yayin da Ƴansanda ke tambayarshi me zai ce game da lamarin sai ya ce yana ba mutane shawara, wanda bai taɓa shiga irin wannan har ba to ya ƙara nisanta kansa da ita saboda ba abu ba ne mai kyau.

Mu Fa Ba Nufinmu Mu Tozarta Sani Lugga Ba Mun Dai Aika Ma Shi Takardar Neman Bayani – Cewar Masarautar Katsina.

Ya kuma ce wannan shine na farko da ya yi bayan da wani ya ba ɓarayin lambarshi suka kirawo shi ya je ya ɗauko su su 7.

Sannan ya ce ya ɗauko su ne daga marabar Musawa ta jahar ta Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram