Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga dokar da zata bada damar gudanar da sahihin zaɓe ta 2022.
Buhari ya sanya ma dokar hannu ne a ranar Juma’ar nan a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
A jawabin sa jim kaɗan bayan rattaba hannun shugaba Buhari ya bayyana cewa a bisa al’ada, ya yi jiran gudummawa ne ko tofa albarkacin bakin ma’aikatu da rassa da cibiyoyin gwamnati da suka ɗauki lokaci mai tsawo suna nazarin dokar da kuma matsalolin da ke tattare da ita kafin a saka hannu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sau Da Yawa Muna Ba Gwamnatin APC Ta Katsina Satar Amsa Amma Basu Amfani Da Ita – In Ji PDP Ta Katsina
Majiyar Jaridar Kakaki Network ta
wato, Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Buhari ya yi amanna cewa, sanya hannu a kan wannan doka zai taimaka wajen samar da sahihin zaɓe wanda kowa zai yi alfahari da shi.
Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, da kakakin majalisar wakilai ta ƙasa, Femi Gbajabiamila, sun halarci bikin sanya hannu ga dokar.