Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce matsalar hare-haren ta’addanci na kara ta’azzara a yankin Arewacin Najeriya.
El-Rufa’i ya yi maganar ne a yayin wata fira da ya yi da BBC inda ya ce wannan matsala ta fi karfin jami’an tsaro duba da yadda babu isassun jami’an tsaron da zasu kawo karshen ta’addanci a kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Sanya Hannu Ga Sabuwar Dokar Da Zata Samar Da Sahihin Zaɓe A Najeriya
Gwamnan ya ce wannan dalilin ne ya sanya shi da wasu gwamnonin jahohi biyar na yankin da ke fama da matsalar tsaron suka yanke shawarar shigowa da jirage marasa matuka wadanda ake dora masu makamai da ake iya sarrafawa daga nesa a cikin kasar domin taimaka ma sojojin saman Najeriya wajen murkushe su.