Mu Fa Ba Nufinmu Mu Tozarta Sani Lugga Ba Mun Dai Aika Ma Shi Takardar Neman Bayani – Cewar Masarautar Katsina.

Masarautar Katsina ta bayyana cewa takardar da ta tura ma Farfesa Sani Lugga ta neman bayani daga gare shi ba ta yi haka ba ne da nufin tozarta shi.

Sarkin yaƙin masarautar Alahaji Ibrahim Ifo ne ya shaida haka a yayin wata zantawarsa da BBC dangane da murabus ɗin da Sani Luggan yayi daga miuƙaminsa na Wazirin Katsina a ranar 23 ga wannan wata na Fabrairu na shekarar 2022.

KARANTA WANNAN LABARIN: Matashi Ya Kashe Kawunsa Bayan Ya Sadu Da Matarsa

Ibrahim Ifo ya ce Masarautar ta aika ma wazirin ne da takardar neman bayani kan wasu kalamai da ya yi a birnin Ilori na jahar kwara.

Ifo ya ci gaba da cewa ana aika ma wazirin da saƙon takardar sai shima ya aiko da takardar ajiye aiki kafin ya bayar da amsa kan bayanin da akka nemi ji daga gare shi.

Sarkin yaƙin ya ce abinda yasa masarautar ta nemi jin ta bakin Lugga saboda kalaman da ya yi a Ilorin sun tayar da hankula a jahar.

Ya kuma ce bai kamata ba wasu abunuwan da ya faɗa a matsayinsa na mai riƙe da babbar sarauta ya kamata duk abin da zai faɗa da ya shafi jama’a ya zama masarauta na da masaniya a kai.

Wazirin na Katsina dai ya yi jawabi ne a wajen wani taro kan matsalolin tsaro da jihar Katsina ke fama da su.

A jawabin na sa ya ce ƙananan hukumomi bakwai ba sa hannun gwamnati kuma hakimai da shugabanni sun yi ƙaura daga wurarensu zuwa cikin birnin Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram