Sabuwar Dokar Zaɓe: Buhari Na Son A Goge Sashen Da Ya Ce Masu Muƙaman Siyasa Su Sauka Daga Kan Mukamansu Kafin Gudanar Da Zaɓe

Shugaban Buhari na Najeriya ya buƙaci Majalisun Dokokin ƙasar su goge sashen da ya hana masu muƙaman siyasa neman takara a cikin sabuwar dokar zaɓen da ya sanya wa hannu a ranar juma’ar nan.

BBC ta ce, Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake sanya wa dokar hannu a fadar Abuja da ke Abuja.

Karanta wannan labarin: Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Sanya Hannu Ga Sabuwar Dokar Da Zata Samar Da Sahihin Zaɓe A Najeriya

Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya buƙaci duk wani mai muƙamin siyasa ya ajiye muƙaminsa kafin ya tsaya wata takara a babban zaɓe.

Wannan na nufin za a tilasta wa wasu manyan jami’an gwamnatin Buhari su sauka daga madafun iko kafin babban zaɓe na 2023.

Buhari ya ce wasu daga cikin tanadin dokar za su haɓaka harkokin zaɓe “kamar 3, 9(2), 34, 41, 47, 84(9), (10), (11) da sauransu”.

“Sai dai abin ba haka yake ba… a sashe na 84 (12) wanda ya shatale masu riƙe da muƙaman siyasa game da zaɓensu da kuma jefa musu ƙuri’a a manyan tarukan jam’iyyu idan ba a gudanar da zaɓen ba cikin kwana 30 kafin zaɓe,” in ji shugaba Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram