Sau Da Yawa Muna Ba Gwamnatin APC Ta Katsina Satar Amsa Amma Basu Amfani Da Ita – In Ji PDP Ta Katsina

Jam’iyyar adawa ta PDP a Katsina ta yi iƙirarin cewa ta sha ba APC satar amsa game da yadda ya kamata ta biya tsoffin ciyamomin ƙananan hukumomin jahar da ta sauke saboda ba a zaɓe su kan ƙa’ida ba kamar yadda gwamnatin APC ɗin ta ce.

Tsohon shuhaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin jahar Katsina, Ibrahim Ɗankaba ne ya bayyana haka a ranar Juma’ar nan a yayin da ya ke tsokaci kan dambarwar da ke akwai akan batun biyan kuɗaɗen tsofaffin ciyamomin ƙananan hukumomin jahar haƙƙinsu da kotun ƙoli ta bada umurnin a biya tun a shekarar da ta gabata.

KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴansanda Sun Ce Sun Kama Wani Direba Da Suke Zargin Yana Ɗaukar Ƴan ta’adda Da Motarsa Ya Kai Su Wurin Da Zasu Saci Mutane A Katsina.

A cikin bayanin na Ɗankaba, ya ce rashin yin biyayya da gwamnatin ta yi ga kotun ta hanyar ƙin bin biyan kuɗaɗen ya sa a yanzu kotun ta sake bayar da wani umrnin rufe asusun ƙananan hukumomin jahar har sai gwamnati ta biya kuɗaɗen daga yanzu zuwa 21 ga watan Maris na shekarar nan ta 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram