Takarar Shugaban Kasa 2023: Atiku Ya Ziyarci Obasanjo A Abeokuta,Don Neman Goyon Bayan Sa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Asabar, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta dake jihar Ogun.

Da misalin karfe 10:10 na safe Atiku ya isa hasumiyar Hilton na Obasanjo inda wani jigon siyasar Ogun ya tarbe shi.

KARANTA WANNAN LABARIN: Nnamdi Kanu Na Fama Da Ciwon Zuciya, Zai Iya Mutuwa A Hannun DSS — inji Lauyan shi

Ziyarar tasa ba ta rasa nasaba da burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Babban mai kalubalantar shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na shekarar 2019, ya yi ta yawo a fadin kasar nan, inda yake ganawa da jiga-jigan ‘yan siyasa domin neman goyon bayan ya mallaki kujerar Aso Rock da ake nema ruwa a jallo a 2023.

Obasanjo ya nada Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 amma duk da haka sun rabu biyu a magriba a wa’adinsu na biyu.

Duk da haka, ya bayyana cewa sun yi sulhu a tsawon shekaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram