Shugaban hukumar kula da ilimin bai-daya ta kasa, UBEC, Dr. Hamid Bobboyi, ya koka dangane da karancin malamai a matakin ilimin bai-daya a Najeriya.
Bobboyi, wanda ya yi wannan furuci mai ban takaici a Legas a ranar Juma’a, ya bayyana cewa, matsalar ta fi kamari a yankin arewacin kasar inda a wasu makarantun ma malami daya ne kawai ke koyarwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Tsaya Gida Ku Ji Da Hayaniyar ASUU Da Ku Afka Ma Yaki – Shehu Sani
Matsalar dai ta saka harkar ilimin firamare da na karamar sakandare na gwamnati a cikin wani mummunan hali da ke bukatar daukin gaugawa.
Jaridar ‘Tribune’ ta ruwaito cewa, shugaban hukumar ta UBEC ya ce, kamar yadda bincike ya nuna, jihohi uku ne suka fi shiga cikin wannan matsala inda kashi 10 na makarantun su ke da malami daya tilo, shi ne shugaban makaranta, wato hedimasta, shi ne kuma malamin dukkanin dalibai daga aji 1 har zuwa 6.
Ko da yake Dr. Bobboyi bai bayyana sunayen makarantun uku ba, ya kara da cewa sauran malamai na ganin ba su samun kulawar da ta kamata, abin da ya sanya su barin aikin domin neman inda za su samu hakan.
Bobboyi dai ya yi wannan bayani ne a lokacin wani taron ganwa da wadanda suka amfana da shirin daukar malaman wucin gadi na gwamnatin tarayya, FTS, na shekarar 2020 da 2021 a jihar Legas da shugabannin makarantu da jami’an hukumar ta UBEC da kuma shugaban hukumar ilimin bai-daya na jihar Legas da dai sauran masu ruwa da tsaki.