Tsohon Mataimakin Shugaban ‘Kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce a shirye ya ke ya tsaya takarar Shugabancin ‘Kasar a kakar zabe mai zuwa ta 2023.
Atiku ya bayyana haka ne ga manema labarai Jim kadan bayan ganawarsa da tsohon Shugaban ‘Kasar ta Najeriya, Olusegun Obasanjo a ziyarar da ya kai domin neman goyon bayansa game da tsayawarsa takarar Shugabancin’Kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zan Samar wa Ƴan Najeriya Aikin yi, Ilmi Da Cigaba – Inji Tinubu
An tambayi Atiku cewa amma ba ya ganin shi yansu ya kwana biyu kuma ga matasa na ta fafutukar a sakar masu ragamar jagorancin kasar? Sai ya ce to ai magana ce ta siyasa don haka matasan su fito a gwada mana a gani.