Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Sa Kai Ne Sun Kashe Wani Bafulatani ‘Yan sanda Sun Kama Su A Katsina

Rundunar Yan sandan jahar Katsina ta ce ta yi nasarar kama wasu mutane biyu da take zargin ‘yan sa kai ne bisa zarginsu da kashe wani Bafulatani.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ne ya gabatar da mutanen ga manema labarai a ranar Alhamis din da ta gabata a farfajiyar hedikwatarsu.

KARANTA WANNAN LABARIN: Sabuwar Dokar Zaɓe: Buhari Na Son A Goge Sashen Da Ya Ce Masu Muƙaman Siyasa Su Sauka Daga Kan Mukamansu Kafin Gudanar Da Zaɓe

Ya ce Mutanen biyu da suka hada da Haruna Sani mai shekaru 37 daga karamar hukumar Kusada da Bishir Mu’azu wanda aka fi sani da kaura, dan shekara 20 daga karamar hukumar Kankia duk a jahar Katsina, sun kama wani Bafulatani da suke zargin barawo ne kuma suka kama shi suka tafi da shi cikin daji suka kashe shi suka sanya shi cikin wata tsohuwar rijiya.

SP ya ce binciken Yan sanda ya gano mutanen biyu kuma su suka nuna ma Yan sanda rijiyar da suka tura shi.

To sai dai mutanen biyu sun ce su ba su kashe shi ba sun dai be bubbuge shi suka tafi inda wadanda suka bari wurin su suka kashe shi kuma suka tura shi rijiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram