Wata Babbar Kotun Najeriya Ta Rufe Asusun Hadin Gwiwa Na Kananan Hukumomin Jahar Katsina.

An samu wata dambarwa tsakanin gwamnatin jahar Katsina karkashi gwamnan jahar Aminu Masari da kuma mutanen jam’iyyar adawa ta PDP a jahar wanda har ta kai ga Kotun ta bayar da umurnin gaggauta rufe Asusun Hadin gwiwa Na kananan Hukumomin Jahar kamar yadda jam’iyyar PDP ta ce.

Jam’iyyar PDP ta bakin shugabanta na jahar Salisu Yusuf Majigiri, ya ce tun lokacin da Kotun ta yanke hukunci akan gwamna Masari ya biya tsofaffin ciyamimin da ya sauka daga kujerunsu hakkinsu suke saurarensa da ya bi umurnin kotu amma gwamnan bai bi ba.

Majigiri ya ce gwamnatin Masarin na ce ta fara biyan kudaden sai dai su kuma a bangarensu sun ce bai biya ba kuma ko wadanda ya ce ya fara biya din bai biya su kan ka’ida ba kamar yadda doka ta ce.

Shugaban PDP ya ce wannan shine dalilin da ya sanya suka sake garzayawa zuwa kotun suka fada mata cewa gwamnan ya ki bin umurnin da Kotun koli ta bata ita kuma kotun ta bada umarnin gaggauta rufe asusun hadin gwiwa na Kananan Hukumomin har sai Masari ya biya kudaden gaba daya daga nan zuwa watan Maris na shekarar nan.

Saidai da muka nemi jin ta bakin jam’iyyar mai mulki ta APC game da batun, Mataimakin Ciyaman na jam’iyyar, Bala Abubakar Musawa, ta musanta cewa kotun ta rufe asusun hadin gwiwar, ta ma kara da cewa wadannan kudaden da jam’iyyar PDP ke magana tana kan biya kuma sannan jam’iyyar ta PDP na neman ta yi masu rinto ne inda ta ke bukatar a biya tsoffin ciyamomin kudaden shekaru 3 sabanin shekara daya watanni da suka dauka suna aiki a ofis.

Musawa ya kara da cewa kawai su abinda suke kallo jam’iyyar PDP din na son ta kawo rudani ne ga zaben da ke tafe na Kananan Hukumomin Jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram