Jigon Jam’iyyar APC na Ƙasa Bola Tinubu yace ƴan Najeriya na buƙatar aikin yi, ilmi da Cigaba.
Ya bada tabbacin cewa zai bayar dasu idan aka zaɓe shi ya zama Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wata Babbar Kotun Najeriya Ta Rufe Asusun Hadin Gwiwa Na Kananan Hukumomin Jahar Katsina.
Yayi jawabi ne a Fadar Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Olanipekun Oyetunji a lokacin tattaunawar sa a Jahar Osun.
A cewar Tinubu “Najeriya da kuka sai a Shekarar 2015 tana da rashin lafiya, amma Jam’iyyar APC tayi magani.
“Muna buƙatar ayyukan yi, ingantaccen ilmi ga yaran mu, muna buƙatar cigaba a Ƙasar mu, muna buƙatar wanda zai iya bada hakan, muna dashi a taken ƙasar mu cewa duk da muna da bambancin al’adu, amma ƴan uwan juna ne.
“Ya zama dole mu zama tsinstiya maɗaurin ki guda, dole mu sani idan jinin da muka sani ne yana gudana a cikin jijiyoyin mu ba tare da la’akari da bambancin addini da al’ada ba. To dole muna da ɗabi’a ta cigaba.