Ba Dan Gidan Abacha Ba Ne Hafsat Ta Aura.

Jaruma a Masana’antar shirya fina-finan Hausa, Hafsat Idris da mahaifin angonta Mukhtar Hassan Hadi wanda ta aura a cikin sirri sun musanta labarin da ake yadawa wanda ke cewa dan gidan marigayi tsohon Shugaban Najeriya ne ta aura.

Sun bayyana haka ne ta hanyar kiran mujallar Fim wadda ita ce ta buga labarin tun da farko, suka ce ba dan gidan Abacha ba ne Hafsat din ta aura.

Fim ta ruwaito cewa, a ranar Lahadin nan ne da safe ta samu labarin cewa Hafsat din wadda ake wa lakabi da “Barauniya ta yi aure a jiya Assabar a asirce.

Auren wanda aka ce an daura a Kano kamar yadda wata kawar Hafsat din wadda ta bukaci Fim din ta boye sunanta ta ce, dan gidan Abacha ne ta aura sai dai ba ta fadi sunansa ba ta dai ce an haife shi a Villa.

Fim ta ce dalilin da yasa ta yarda da labarin saboda ta ga yadda kusancin kawar tata ya ke da ita, sannan kuma sun nemi jin ta bakin Hafsat din abin bai yiwu ba.

Sai dai bayan labarin ya fita sai ita amarya Hafsat da mahaifin mijin nata suka kira mujallar Fim ta waya suka musanta batun har ma ita Hafsat din ta ce tana bukatar a gggauta goge labarin.

Daga bisani kuma mujallar Fim ta kirawo kawar Hafsat din da ta fada mata cewa dan gidan Abacha ne ta aura sai kawar ta ce, ita Hafsat din ce ta fada ma ta sai dai ko dan dangin su Abacha ta ke nufi amma dai ita haka Hafsat din ta fada ma ta don haka in ma kuskure ne ita ta yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram