Ganduje Ya Shirya Yi Ma Shanu Milyan 1 Allurar Rigakafi

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje, ta bayyana cewa ta ɗauki ma’aikatan kiwon lafiyar dabbobi 220 domin bunƙasa fannin kiwon dabbobi da kuma gudanar da aikin jagorantar makiyaya a ayyukansu.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da haka a ranar Asabar din na na yayin bikin ƙaddamar da allurar riga-kafin shanu da ƙananan dabbobi a fadin jahar.

KARANTA WANNAN LABARIN: A Kasa A Tsare A Raka A Jira. Kalma Ce Da APC Ta Yi Amfani Da Ita Ta Yaudari Mutanen Najeriya – Shugaban Matasan PDP Na ‘Kasa

Ganduje ya ce gwamnatinsa na da kudirin yi wa shanu miliyan ɗaya allurar rigakafi a bana kyauta a fadin jihar.

Gwamnan ya kuma buƙaci makiyaya a jihar Kano da su baiwa gwamnatinsa haɗin kai domin bunƙasa harkar kiwon dabbobi a jihar.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta bullo da matakan sauya al’adar daga zamantakewar al’adu zuwa cigaban tattalin arziki.

Kakaki Network ta ruwaito cewa, a wata sanarwa da Mai baiwa Gwamnan shawara a kan kafofin sada zumunta na zamani, Salisu Muhammad Mati ya fitar ta bayyana cewa Gwamna Ganduje yace a bara mun yi nasarar yi wa Shanu 703 allurar rigakafi da jiragen ruwa da awaki 664 wanda kusan kashi 80 cikin 100 na abin da aka yi niyya kuma ba mu samu bullar cutar a jihar ba wadda ta bai wa makiyaya damar samun riba mai yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram