Tsohon Ministan ma’aikatar Al’adu da yawon bude ido na Najeriya, Femi Fani Kayode, ya bayyana cewa in ba a yi taka tsantsan ba game da rikincin Rasha da Ukraine lamarin ba zai zama mai sauki ba.
Kayode ya bayyana haka ne a saman shafinsa na Twitter, inda ya ce rikincin na iya zama silar afkuwar yakin duniya na 3.
Tsohon Ministan ya ce bai kamata mutane na goyon bayan wani bangare ba ba tare da ji daga bangarorin kasashen biyu ba.
Ya ce babbar matsalar da da yawa yan Najeriya da Mutanen Afirika da ma na kasashen turai dun ba su ji bayani ba daga kowanne bangare na kasashen.