Shugaban ‘Kasar Ukraine Ya Yarda Zai Tattauna Da ‘Kasar Rasha

Shugaban ‘Kasar Ukraine Volodymyr Zelinsky ya ce ya yarda zai sasanta da Rasha a wani wuri kan iyakar Ukraine da Belarus

Shugaba Zelensky ya ce a tattaunawar da ya yi da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, Ukraine ta amince ta gana da Rasha ba tare da wani sharaɗi ba a kan iyakar Ukraine da Belarus a kusa da kogin Pripyat.

KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Rasha Ya Umarci Dakarunsa Da Ke Kula Da Makaman Nukiliya Su Zama Cikin Shirin Ko Ta Kwana

BBC Hausa ta ayyano cewa, Shugaban ya ce Mista Lukashenko ya ce ya ɗauki alhakin tabbatar da dakatar da shawagin dukkanin jiragen sama, masu saukar angulu da masu kakkabo makamai mai linzame lokacin ziyarar domin tattaunawar tsakanin ɓangarorin biyu.

A da da farko dai Msita Zelensky ya yi watsi da tayin Rasha na hawa teburin tattaunawa da Belarus. Ya ce ya fi buƙatar a tattauna a wata ƙasa saɓanin Belarus.

Belarus babbar aminiyar Rasha ce a yaƙin da take da Ukrainer.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram