Shugaban ‘Kasar Rasha Vladimir Putin ya umurci kwamandojin sojin ƙasar su shirya dakarun Rasha masu kula da makaman nukiliya su kasance a cikin shiri.
Putin ya ssnar da hakan ne a yayin wata tattaunawa a fadar Kremlin wanda ministan tsaro da kwamandan sojojin kasar suka halarta.
KARANTA WANNAN LABARIN: In Ba A Yi Taka Tsantsan Ba Rikincin Rasha Da Ukraine Zai Haifar Da Yakin Duniya Na Uku – Femi Fani Kayode
BBC Hausa ta ruwaito cewa, shugaba Putin ya ce manyan jami’an ƙasashen yammaci sun yi zafafan kalamai kan Rasha.
Sannan kuma ya kira takunkuman da kasashen yammaci suka ƙaƙabawa kasarsa ta sa a matsayin haramtattu.