Yansanda Sun Kama Wani Tsoho Mai Shekaru 60 Da Laifin Sha Da Sayar Da Miyagun Kwayoyi

Rundunar Yan sandan jahar Katsina ta kama wani dattijo mai shekaru 60 mai suna Ilyasu Abdullahi da zargin sha da kuma sayar da miyagun Kwayoyi a Katsina.

Dattijon a yayin da kakakin rundunar Yan sandan jahar SP Gambo Isah ya ke tambayarshi akan abinda ake tuhumuarsa da shi, ya amsa laifinsa.

KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje Ya Shirya Yi Ma Shanu Milyan 1 Allurar Rigakafi

Abdullahi wanda ya je gidan yari kusan sau 4 da kuma zuwa hannaun jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi, NDLEA kimanin sau 10, ya ce in Allah ya yarda daga yanzu ya daina ta’ammali da miyagun Kwayoyi.

A halin da ake yanzu haka wasu daga cikin yayanshi na cikinsa suna shan kwayoyin kamar yadda ya ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram