Dalilan Da Suka Sa Putin Ya Ba Dakarunsa Umarnin Dana Makaman Kare-dangi.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin ‘kasar Rasha, Dmitry Peskov, ya ce umarnin da Shugaba Putin ya bayar ranar Lahadin da ta wuce ga dakarun ƙasar na su kasance cikin shirin amfani da makaman ƙasar ciki har da na Nukiliya martani ne ga Sakatariyar harkokin Wajen Birtaniya Liz Truss.

Peskov ya ce akwai kalamai na rashin kamun kai waɗanda ba za a lamunta ba, da ke fitowa daga bakin wakilai daban-daban na ƙasashen Turai game da fito-na-fito tsakanin NATO da Rasha, ciki har da wanda ministar harkokin wajen Birtaniyar ta yi.

KARANTA KUMA: Dankaba Ba Ya Tausayin Al’ummar Katsina Tunda Har Ya Nemi Kotu Ta Rufe Asusun Hadin Gwiwa Na Kananan Hukumomin Jahar – Sharhi

Ministan tsaro na Birtaniyar, Ben Wallace, ya ce Birtaniya ta kalli matsayin na Rasha a kan makaman kare-dangi, kuma ta lura cewa babu wani sauyi na a zo a gani a kai.

BBC ta ce kakakin ya ce Mista Putin, yana son ya nuna karfin Rasha ne, ta hanyar ambato shirin ko ta kwana na amfani da makaman nukiliyar na kasarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram