A yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar karancin man fetur a jihar Oyo, a ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta yi barazanar rufe wasu gidajen mai na mambobin kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN da suka ki sayar da litar ma akan Naira 165.
Wakilinmu ya rawaito cewa, wasu ‘yan kasuwa na sayar da man fetur tsakanin Naira 200 zuwa 250 kan kowace lita, musamman ma da daddare.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban ‘Kasar Ukraine Ya Yarda Zai Tattauna Da ‘Kasar Rasha
Hakance tasa karancin man fetur ya sanya masu ababen hawa na kasuwanci suka kara kudin shiga da kashi 100 cikin 100 na hanyoyin shiga da kuma tsakanin jihohi.
Da yake zantawa da manema labarai a Ibadan ranar Lahadi, Kwamandan NSCDC na jihar, Adarelewa Michael Akintayo ya sake nanata shirye-shiryen rundunar na sanya takunkumi ga gidajen man da suka yi kuskure.
Ya bayyana cewa wasu ‘yan kasuwa na cin gajiyar karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan don tayar da farashin mai.
Kazalika hakance tasa Majiyar Jakadiya zagayawa wasu daga cikin sassan gidajen sayar da man fetur dake wajen jihar kano da sanin yadda farashin man Fetur ke gudana.
Haka Zalika, Majiyar Jakadiya ta yada zango a karamar hukumar Wudil dake jihar kano inda ta tararar da wasu gidajen sayar da man fetur ana sayar da litar man akan naira 228,yayin da a wajen ‘yan bunburutu ake sayar dashi akan naira 300 kan kowacce lita wani wajen ma sama da haka.
Kazalika a karamar hukumar Albasu wasu gidajen man ma basa budewa wanda hakan yasa fasinjoji suke shan matukar wahala tare da biyan kudin sufuri mai tsada ga wadanda suke da kudin wadanda kuma basu dashi suna tikar tafiya ne da kafafun su.