Birtaniya Ba Ta Yarda Ta Tura Dakarunta Ukraine Don Yin Taho Mu Gamu Da Rasha Ba

Firaiministan Burtaniya Boris Johnson ya ce ba za su aika sojojisu Ukraine don ƙalubalantar Rasha da ke mamayar ƙasar ba.

Johnson ya ce ko ma wane mataki ne za su ɗauka za su ɗauke shi ne da haɗin guiwar ƙungiyar tsaro ta NATO, kuma shima ɗin bai wuce na girke dakaru a ƙasashen da ke ƙarƙashin ƙungiyar da ke maƙotaka da Rasha ba.

KARANTA KUMA: Yadda Wasu Gungun Matasa Da Ake Zargin Barayi Ne Suke Wawushe Gidaje Da Shagunan Jama’a A Katsina

‘BBC ta ce, ya ce ‘Ina son dai in kawo karshen dukkan waɗannan maganganu da ake yi, ba zai yiwu mu yi yaƙi da Rasha ba, matakan da muke ɗauka yanzu na ƙare kanmu ne, ba ma sn mu ɗauki wani mataka da zai iya dagua al’amura” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram