Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta sake zama teburin tattaunawa da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya.
Taron ranar Talata shine karo na biyu da akayi, tun bayan da Ƙungiyar ta ayyana yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya.
Malaman suna so a kara masu walwalar su, da farfaɗo da Jami’o’in Najeriya, da kuma basu gashin kansu da sauran buƙatu.
KARANTA KUMA:Harin Rasha Ya lalata Tirken GidanTalabijin Na Kyiv, In ji Hukumomi A Ukraine
Wakilan Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya da suka halarci taron, sunce basu wani ra’ayin sake sa hannu akan wata yarjejeniya fahimta.
Suna buƙatar ayi aiki akan yarjejeniyar da akayi a baya.
Haka zalika, Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya bayyana fatan cewa zasu shawo kan lamarin.
Dukkanin ɓangarorin guda biyu sun ki amincewa akan wanda ke kawo tsaiko akan tabbatar da tsarin biyan Albashi na suka ɓullo dashi na UTAS.
A yayinda Ministan ya bayyana cewa Ƙungiyar na kawo tsaiko akan amfani da tsarin UTAS da Hukumar NITDA, Malaman sun jajirce akan cewa NITDA bata shirya karɓar su ba.
Rashin amincewa akan tsarin biyan Albashi yana ɗaya daga cikin Malaman suka lissafo wanda ya sanya suka shiga yajin aiki.
Harin Rasha ya lalata Tirken gidan talabijin na Kyiv, in ji Hukumomi a Ukraine
Dakarun sojin Rasha sun kaddamar da hari kan Tirken Na’ura Talbijin a Birnin Kyiv Wanda ya kawo cikas ga yada shirye-shirye, kamar yadda Mai bada shawara kan harkokin kasashen waje na Ukraine Anton Herashcenko ya bayyana
Sai dai wata kafar Talbijin ta cikin Gida a Ukraine ta bayyana cewa, dayuwar komai ya dai daita.
Jaridar The Kyiv Independent dake yada labarai ta harshen Turancin a kasar Ukraine ta bayyana cewa, Kafar Talbijin din na kasar ya tsaya cak da yada Shirye-Shiryensa, sakamakon mummunan harin daga dakarun kasar Rasha.
Sai dai har kawo hada wannan rahoton Kafar Talbijin na Al-Jazeera Bai iya tabbatar da wadannan ikirariba da Kafafen yada labarai na kasar Ukraine ke yi.