Shugaban Ukraine Voladymyr Zelensky ya yi kira ga shugaban Rasha Vladimir Putin da ya dakatar da kai wa kasarsa hari.
Yana magana ne a yayin da ake yunkurin tattaunawar sulhu ta biyu da ake sa ran bangarorin biyu za su yi.
KARANTA KUMA: Buhari: Dole Masu Garkuwa Da Yan Makaranta Su Dandana Kuɗarsu
Ya ce matsawar ana son nuna wa duniya cewa tattaunawar sulhun na da muhimmanci, to ya kamata a daina kai wa juna hare-hare.
BBC ta ruwaito cewa, Yayin wata tattaunawar haɗin guiwa da CNN da Reuters, shugaba Zelensky ya ce wa Putin ”Ka dakatar da kai wa jama’a hari, ka zo mu zauna a teburin sulhu a sasanta”