NDLEA ta Shirya Dukkanin Takardun Gurfanar da Abba Kyari

ukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta shirya Takaddun gurfanar da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar Abba Kyari a gaban kotu.

Za’a gurfanar da Kyari tare da wasu mutane shida da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Sauran wadanda ake tuhumar dai jami’an ‘yan sanda ne na Intelligence Response Team (IRT) na Sufeto-Janar na ‘yan sanda, ACP Sunday J. Ubia, ASP Bawa James, Insfecta Simon Agirigba and Insfecta John Nuhu.

Sauran wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi da aka kama a filin jirgin saman Akanu Ibiam da ke Enugu, sun hada da: Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

KARANTA WANNAN LABARIN:

Shugaban Ƙasar Mozambique ya sallami Ministocin sa guda 6

Za a gurfanar da su ne a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar 7 ga Maris.

Hukumar NDLEA ta bayyana cewa tana ta kama Kyari ne bayan da ta samu faifan bidiyo da ke nuna yadda ya ke tattaunawa da masu bincikenta kan cinikin kwayoyi.

An kama sauran wadanda ake tuhumar ne a ranar 19 ga watan Janairu a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu kuma sun amsa cewa masu safarar miyagun kwayoyi ne.

Tun da farko a ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa an fara shirin mika Kyari ga Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram