Shugaban Ƙasar Mozambique ya sallami Ministocin sa guda 6

Shugaban Kasar Mozambique Filipe Nyusi ya Kori Ministoci shida harda na fannin kula da kudin kasar, a wani yunkurin na samun dai-daito kamar yadda Ofishin Shugaban Kasar ya bayyana.

Sanarwar bata fayyace Wani dalili daya ba da yasa Shugaban Kasar ya dauki irin wannan tsatsauran Mataki kan Ministoci nasa, kana bai bayyana lokacin da zai maye gurbinsu ba.

Wannan dai shine karo na biyu da Shugaban Filipe ke yin sauye sauyen a majalissar zartaswarsa, cikin watannin baya bayan nan.

Sauran da Shugaban ya kora sun hada da ministocin ma’adinai da makamashi, ayyukan gwamnati, gidaje da na ruwa, da dai sauran su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram