Idan Bukola Saraki Ya Zama Shugaban ‘Kasa Najeriya Za Ta Samu Gwarzon Shugaba Kamar ‘Yar’adua – In Ji Farfesa Haiye

Wani tsohon Jakadan Najeriya, Sanata kuma Farfesa, Iyorwuese Hagher, ya bayyana marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, a matsayin nagartacce kuma adalin shugaba wanda ya kawo gaggarumin ci gaba a jihar Katsina da Najeriya baki daya.

Farfesan wanda kuma tsohon minista ne, ya yi fadi hakan ne Katsina a yayin da ya jagoranci tawagar mambobin kwamitin neman goyon bayan bai wa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Ambassada Hagher, ya ce, a halin da Najeriya take ciki yanzu, akwai matukar bukatar dawowar irin shugaba Umaru Yar’adua kuma Sanata Bukola Saraki shi ne ya cancanci wannan matsayi ta la’akari da ilimin sa da gogewar sa ta fuskar siyasa da shugabanci gami da kyakkyawar alakar sa da marigayi Umaru Yar’adua.

Ya kara da cewa, dukkanin mutanen 2 kuma sun yi gadon shugabanci da siyasar da ta kara bai wa ‘yan Najeriya ‘yanci da tabbatar da ci gaban mulkin dimokuradiyya a kasa baki daya.

Ya ce, kowa ya san yadda Yar’adua da Saraki suka tsaya a kan gaskiya komai dacin ta domin tseratar da al’umma daga shiga halin kunci da kaka ni-ka-yi a jihohin su da kasa baki daya.

Hagher ya kara da cewa abin kunya ne a ce jihar Katsina ce ke da gwamna da shugaban kasa duk ‘yan jam’iyyar APC mai mulki amma ba ta da kwanciyar hankali kuma babu wani ci gaban a zo a gani a jihar.

Ya kuma bayyana takaicin sa a kan yadda jihar Katsina ke matsayin ta biyu wajen yawan yaran da ba su zuwa makaranta a fadin Najeriya duk da dimbin kuri’un da ta bai wa jam’iyya mai mulki ta APC a dukkanin matakai.

Tsohon ministan wanda ya fito daga karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue ya bayar da tabbacin cewa jinin Umaru Yar’adua ne a cikin jikin Bukola Saraki don haka akwai bukatar a ba shi dama ta yadda zai iya ginawa tare da farfado da ayyukan alkhari na marigayi Yar’adua.

A jawabin sa, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, Salisu Majigiri, ya ce, duk da hayagagar da ake, babu aiki ko da na naira bilyan 3 da gwamnatin APC ta yi a jihar Katsina da ya kai matakin kaddamarwa a shekaru 7 din da ta yi tana mulki.

Ya ce, jam’iyyar PDP a jihar Katsina na aiki tukuru domin kara hada kawunan ‘ya’yan ta, musamman ganin zaben na 2023 na kara karatowa, ga kuma zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar a cikin watan Afrilun 2022.

Majigiri ya yi amannar cewa jam’iyyar PDP ce ke da nasara a dukkanin zabubbukan da ke tafe ta la’akari da tarihin da ta kafa wajen ciyar da kasa gaba, inda ya ce APC ba ta ma kama hanyar samun irin wannan nasara ba.

Tawagar nema wa Sanata Bukola Sarakin goyon baya ta hada da jiga-jigan ‘yan siyasa da suka hada da tsohon gwamnan jihar Kwara, Shaba Lapiagi da tsofaffin sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram