Babbar Jam’iyyar adawa PDP a jahar Katsina ta sha alwashin samar da walwala da jin dadi da kwanciyar hankali ga al’ummar Katsina.
Manyan jigajigan jim’iyyar ne suka fadi haka a yayin da kowa ke tsakaci kan halin da Jama’a ke ciki a jahar Katsina kamar yadda suka ce.
KARANTA KUMA: Ukraine Ta Buƙaci Jamus Data Taimaka Masu Da Yankunan Yaƙi na Jiragen Ruwa
Jam’iyyar ta bada tabbacin cewa idan Allah ya bata nasara a zaben kananan Hukumomin jahar da za a gudanar a watan Afrilu mai zuwa.
Wadan nan bayanai mabanbanta na fitowa ne daga bakunan manyan jam’iyyar a yayin taron bayar da tuta ga yan kararta tun daga matakin kansiloli zuwa dan takarar Shugaban karamar Hukumar Katsina da ya gudana a farfajiyar hedikwatar jam’iyyar da ke Katsina.
PDP ta yi ikirarin cewa idan ta dawo kan mulki Mutanen Katsina ba wanda zai kara sanya kayan gwanjo ko kuma yagaggin kaya.
Sannan ta bada tabbacin samar da tsaro da walwala.