Rikicin Russia da Ukraine: Kashi Na Farko Na Ƴan Najeriya Sun Isa Abuja

A safiyar yau Juma’a ne kashi na farko na ƴan Nijeriya da aka kwashe daga birnin Bucharest na ƙasar Romania su ka sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Mutanen da a ka kwaso daga Ukraine sakamakon mamayar da Russia ta yi a ƙasar Ukraine sun nemi mafaka a Romania.

KARANTA WANNAN LABARIN: Idan Bukola Saraki Ya Zama Shugaban ‘Kasa Najeriya Za Ta Samu Gwarzon Shugaba Kamar ‘Yar’adua – In Ji Farfesa Haiye

Gwamnatin taraiya ta baiwa kamfanin Max Air da Air Peace kwangilar kwashe ƴan Nijeriya da su ka maƙale a kan dala miliyan 8.5, bayan da a ka buƙaci su gudu zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Poland, Hungary, Romania da sauransu.

Yayin da Air Peace ba zai iya tashi daga Najeriya ba kamar yadda aka tsara, saboda wasu matsaloli, jirgin Max Air ya tashi daga Abuja zuwa Bucharest, a ranar Alhamis, kuma yanzu ya dawo da rukunin farko.

Jirgin mai lamba 747-400 mai lambar rijista 5N-HMM ya sauka a filin jirgin ne da karfe 06:11 na safiyar yau, kamar yadda wani jami’in kamfanin ya tabbatar wa wakilinmu.

Rahotanni sun baiyana cewa gwamnatin taraiya ta bada dala 100 ga kowanne ɗan ƙasar da a ka dawo da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram