Tinubu: Najeriya Na Buƙatar Shugaban Da Zai Samar Da Haɗin Kai, Tsaro Da Tattalin Arziki

Jagoran Jami’yar APC na Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a jiya Alhamis ya ce ya shiga takarar shugaban ƙasa ta 2023 ne domin ya samar da ƙwarin gwiwa a zuƙatan ƴan Nijeriya da kuma samar da canjin da ƙasar ke buƙata.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas ɗin ya faɗi hakan ne a Ekiti a yayin ziyarar tuntuɓa zuwa ga Masarautar Ekiti.

A cewar Tinubu, Nijeriya na matuƙar buƙatar shugaba wanda zai kawo haɗin kai tsakanin ƴan ƙasa, ya magance matsalolin tsaro ya kuma haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce ya kawo ziyarar tuntuɓa ɗin ne ga masarautar domin baiyana musu buƙatar sa ta tsaya wa takara da kuma neman albarkacin su a matsayin su ma iyayen ƙasa.

Tinubu ya ƙara da cewa ya kawo ziyarar ne ga masarautar sabo da girmama al’ada.

“Mun daɗe muna fafutukar samun domokraɗiyya. To gashi mun same shi amma har yanzu dimokuraɗiyyar mu ba ta daidaita ba.

“Ya kamata a ce zuwa yanzu mun samu harkar noma mai inganci har mu riƙa noma abinci mu na kai wa wasu ƙasashen.

“Mu ku ka zaɓi mu yi dimokuraɗiyya, sabo da haka dole mu tashi tsaye mu inganta shi,” in ji Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram